fbpx
Monday, March 1
Shadow

Bafulanin da ya saba satar mutane a bashi Miliyoyi ba zai taba dainawa dan haka a kasheshi kawai>>Gwamna El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa baahi da ra’ayin yin sulhu da ‘yan Bindiga.

 

Ya bayyana hakane a hirarsa sa BBChausa inda yace duk wanda yake ganin Bafulatanin da ya saba sai ya shekara ya ga Dubu 100,000 zuwa Dubu 200,000 a shekara amma yanzu ya sace mutum a bashi Miliyoyin wai zai tuba yana yaudarar kansa ne.

 

Gwamna El-Rufa’i yace ba zasu taba daunawa b dan haka a yakesu kawai shine Mafita. Yace banban cin ra’ayin da suka samu da sauran wasu gwamnonin yankin kenan shiyasa aka kasa kawo karshen matsalar.

 

Gwamna El-Rufa’i da yake magana akan shigar Sheikh Gumi daji yana tattaunawa da Fulanin, yace sun yi magana da Gumi kuma ya gaya masa cewa Fulanin nan basu da addini dan haka shi bashi da ra’ayin a yi sulhu dasu. Gwamna El-Rufai da yake maganar Diyya, yace babu wata diyya da zaa biyasu, yace su da suka shiga suka kone gidajen mutane da kashe su sune suke neman diyya?

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *