Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa, bai kamata a tsige shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba.
Ya bayyana hakane yayin ziyarar da ya kai jihar Kwara.
Yace duk da yasan sanatocin na da dalilansu na son daukar wannan mataki sanan kuma matsalar tsaro ta yi yawa, amma abune wanda ya kamata a yi nazari kamin aiwatar dashi.