fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Bai kamata gwamnati ta ajiye ‘yan Boko Haram, ‘yan ta’addan Ansaru da kuma ‘yan bindiga a kurkuku guda ba domin zasu hada kazamar tawaga, cewar Shehu Sani

Tsohon sanatan jihar Kaduna, Shehu Sani ya sake yin tsokaci akan harin da ‘yan ta’addan ISWAP suka kaiwa gidan kurkuku na Kuje daka babban birnin tarayya.

A ranar talata ne ‘yan ta’addan suka kaiwa gidan kurkukun hari inda suka kashe mutane da dama kuma mutanen gidan guda 900 suka tsere abinsu, amma an kamo wasu, sannan wasu kuma sun dawo da kansu.

Shehu Sani ya bayyana cewa dama bai kamata gwamnatin ta ajiye ‘yan Boko Haram da ‘yan ta’addan Ansaru da kuma ‘yan bindiga ba duk a kurkuku guda.

Karanta wannan  Rundumar sojin sama sun hallaka shugaban 'yan ta'addan Boko Haram da tawagarsa a jihar Maiduguri

Saboda yace hakan babban hadari ne kuma dole zasu wata kazamar tawaga a tsakaninsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.