Darektan kungiyar dake kare hakkin bil’dama ta SERAP, Kolawole Oluwadare yayi kira ga hukumar zabe ta INEC cewa ta tsawaitawa mutane lokaci su cigaba da yin rigistar katin zabe.
Inda yace kamata yayi ace ba za’a daina yiwa ‘yan kasa rigistar katin zabe ba har sai ana sauran kwanaki 90 ga zaben.
Kuma yace hukumar ta karawa jam’iyyu lokacin da zasu gudanar da zabensu na fidda gwani amma taki karawa masu yin rigistar katin zaben.