Rahotanni daga AFP sun tabbatar da sake kaiwa Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum hari a yunkuri na 2 da yayi na shiga garin Baga.
A wannan karin harin yayi Muni dan Rahoton ya bayyana cewa an kashe sojoji da ‘yansanda da kuma ‘yan banga da dama.
Channelstv ta ruwaito cewa, Gwamna Zulum ba ya cikin tawagar da aka kaiwa harin saboda ta jirgin sama ya je Baga kuma har yayi Sallar Juma’a tare da sojoji . Zuwa yanzu dai babu wani bayani da ya fito daga gwamnatin jihar Borno kan harin.
A baya da aka kaiwa Gwamna Zulum hari a hanyarsa ta zuwa Baga ya alakanta hakan da zagon kasa, inda wasu sukawa hakan fassarar da cewa sojojinne gwamnan yake zargi. Hakan yasa Hukumar sojin ta yi bincike inda tace harin kalar na Boko Haram ne dan ko yanda ake harbin bindiga yayin harin babu kwarewa a cikinsa.
Sojojine yanzu a garin Baga, kuma gwamna Zulum na kokarin ganin cewa mutanen garin sun koma muhallansu shiyasa yake kokarin ganin ya kai ziyara dan ganin irin tsarin yanda garin yake.
A baya, Gwamnan yayi wata hira da BBC inda ya bayyana cewa, harin da aka kai masa bai razana ba, kuma ga dukkan alama wannan yunkuri na sake shiga Baga ya tabbatar da waccan magana ta gwamnan.
Gwamnan dai na tsammanin karbar Wasu ‘yan Gudun hijirane da zasu koma Baga, kamar yanda Majiyar ta tabbatar.