fbpx
Monday, December 5
Shadow

Baka makara ba, zaka iya gyara Najeriya>>Afenifere ga Shugaba Buhari

Kungiyar kare muradun yarbawa ta Afenifere ta bayyanawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa, matsalar tsaron dake fuskantar Najeriya zai iya gyara ta idan ya tashi tsaye.

 

Kungiyar ta gayawa shugaba Buhari cewa bai makara ba.

 

Tace matsalar tsadar rayuwa, rashin aikin yi, rashin tabbas, da rashi kula ne ya jefa Najeriya halin da take ciki.

 

Sakataren kungiyar, Mr. Jare Ajayi ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar.

 

Kungiyar tace harin da aka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna babban abin kunyane ga Najeriya.

Karanta wannan  Hotunan makaman da sojojin Najariya suka kwace daga hannun 'yan Boko Haram

 

Tace hakan ya jefa tsoro sosai a zukatan ‘yan Najeriya.

 

Kungiyar tace jihohin dake son kafa jami’an tsaronsu ya kamata a karfafa musu gwiwa dan magance matsalar tsaro.

 

Hakanan ta bayar da shawarar a dawo da tsaffin sojojin da suka yi ritaya su taimaka a yaki ‘yan Bindigar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *