Dan takarar shugabancin kasar Amurka, Joe Biden yayi ikirarin cewa bakar fata ne ya kirkiro gulaf din wutar Lantarki da ake amfani dashi.
Ya bayyana hakane a ziyarar da yakai Kenosha, Wisconsin dake kasar inda ya ziyarci iyalan bakar fata, Jacob Blake da ‘yansanda suka harba sau 7.
Ya bayyana cewa idan ya zama shugaban kasa zai yi kokarin gyara akan dokar nuna kabilanci.