fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Bama Zawarcin Goodluck Jonathan >>APC

Jam`iyyar APC mai mulki a Najeriya ta musanta cewa tana zawarcin tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan domin ya tsaya mata takarar shugaban ƙasa a zaɓe mai zuwa na shekarar 2023.

A makon da ya wuce ne wasu rahotanni suka ce wasu gwamnonin APC daga arewacin ƙasar na kai gwauro da mari wajen ganin Goodluck Jonathan ya samu takarar domin dama ɗaya kawai yake da ita ta yin shugabanci na shekaru huɗu, alabashi mulki ya sake komawa arewa.

Sai dai jam`iyyar ta ce a ƙashin gaskiya wasu ne kawai suke ƙirƙirar irin wannan labari, wanda babu ƙanshin gaskiya a cikinsa.

Mai Mala Buni, shi ne shugaban riƙo na jam’iyyar APC, kuma gwamnan jihar Yobe, ya shaida wa BBC cewa: “Ba maganar wani zawarcin Jonathan a halin da ake ciki, wataƙila wadanda suke irin wadannan magaganu akwai tsoro a zukatansu”.

Ya ƙara da cewa “ko da mutum na son kafa hujja ne da ziyarar da muka kai masa yayin bikin zagayowar ranar haihuwarsa, to mun je ne a matsayinsa na tsohon shugaban Najeriya don haka ziyararmu ba ta da wata alaƙa da siyasa.”

Sai dai duk da wannan barranta kai da shugaban jam’iyyar ya yi game da waɗannan rahotanni, bai gushe ba, sai da ya yabawa tsohon shugaban ƙasar Good Luck Jonathan, harma ya kira shi a matsayin ”Uban ƙasa, kuma mai son zaman lafiya” saboda amincewa da ƙaddara da kuma miƙa mulki da ya yi, lokacin da ya sha ƙasa a zaɓen 2015.

Yanzu haka dai tuni manyan ƴan jam’iyyar ta APC da ake kyautata zaton za su tsaya takara a zaɓen shekarar 2023 suka fara wasa wuƙarsu, yayin da ya rage kusan shekaru uku a gudanar da zaɓen.

Masana na ganin cewa za a sha gwa-gwa-gwa wajen neman tikitikin takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar, la’akari da cewa akwai wasu manya da suka dafawa shugaba Muhammadu Buhari duk da suna da sha’awar shugabancin, amma a yanzu ana neman watsa musu ƙasa a ido.

Baya ga haka akwai kuma batun da wasu a jam’iyyar ke yi na cewa ya kamata a miƙa takarar ga kudancin Najeriya don suma su ɗana, tunda shugaba Muhammadu Buhari da ya fito daga arewa ya yi shekaru takwas.

Akwai gaggan ƴan siyasa a jam’iyyar ta APC ciki har da gwamnoni daga arewa dake ganin hakan a matsayin gurguwa dabara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.