Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, sam maganar dauko sojojin haya su yaki ‘yan Bindiga ba abune me yiyuwa ba.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, idan sojojin Najeriya sun gaza, shi da sauran gwamnonin Arewa maso yamma zasu dauko sojojin haya daga kasar waje su zo su kashe ‘yan Bindigar.
Saidai a martanin da gwamnatin tarayya tayi ta bakin ministan yada labarai, Alhaji Lai Muhammad, tace, yaki ds ‘yan Bindiga akwai wahala saboda yanda dazukan Najeriya ke da surkuki.
Yace kuma ayyukan da sojojin Najeriya zasu yi sam ba daya suke da wanda sojojin haya zasu yi ba.