Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, bata ce zata yi karin Albashi ba.
Hakan ya fito ne daga ma’aikatar Kwadago inda ma’aikatar tace an yiwa ministan Kwadago, Chris Ngige mummunar fassara ne.
Kakakin ma’aikatar Olajide Oshundun a sakon daya baiwa manema labarai tace Ministan na nufin Alawus din ma’aikatane za’a duba ba wai maganar karin Albashi ba.
Yace gwamnati ba zata yi karin albashi ba ba tare da sanin kungiyoyin kwadago ba.