fbpx
Friday, February 26
Shadow

Bamu da niyar kara farashin mai a watan Fabrairu – NNPC

Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya musanta shirin karin kudin mai daga watan Fabrairu.

Babban Manajan Rukunin Kamfanin NNPC, Rukunin Harkokin Jama’a, Dakta Kennie Obateru ya ce, Kamfanin na NNPC bai kara kudin mai ba kamar yanda ake sayar da kowace lita daya akan N162.

Ya kara da cewa, yana da tabbacin cewa NNPC ba zai yuwu ta kara farashin man a watan Fabrairu ba.

Yace; Muna da isasshen mai na kusan kwana arba’in da wani abu, Idan kuma masu gidanjen mai suna kara farashin to ya kamata Hukumar DPR ta dauki kwararan matakai cikin gaggawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *