Sanata Kabiru Marafa daga jihar Zamfara ya musanta Rahoton dake cewa shi da Tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari sun koma jam’iyyar PDP.
Ya bayyana hakane ga kafar Tambari wadda jaridar yanar gizo ce ta jihar.
Sanata Marafa yace abinda ya sani shine suna tattaunawa da jam’iyyu da dama da suke zawarcinsu amma ba’a cimma matsaya ba.
Yace amma lallai zasu fita daga APC saboda rashin adalcin da aka musu.
Shugaban jam’iyyar PDP na Zamfara ne dai a jiya ya bayyanawa manema labarai cewa tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari ya koma PDP.