Bamu nemi a soke zaɓen Kano ba – Masu sanya ido kan zaɓe
Gamayyar ƙungiyoyi da suka sanya ido a zaɓen Gwamnan Kano sun nemi jama’a su yi watsi da wani labari da ake yaɗawa wai sun nemi a soke zaɓen Kano.
Ƙungiyoyin sun ce ba su da alaƙa da kowace jam’iyya su suna aiki ne don jama’a.
Sun kuma ce za su ɗauki mataki kan waɗanda suka yi amfani da sunansu wajen yaɗa labarin ƙarya.