fbpx
Tuesday, May 17
Shadow

Bamu yadda da daga zaben 2023 ba>>Dattawan Arewa da Ohanaeze Indigbo

Kungiyoyin Dattawan Arewa ta NEF da Ohanaeze Indigbo ta kare muradun Inyamurai ta sun bayyana cewa, basu yadda da daga zaben shekarar 2023 ba.

 

Chief Afe Babalola, SAN ya bayar da shawarar daga zaben shekarar 2023 inda yace a kafa gwamnatin rikon gwarya sannan daga baya bayan an canja kudin tsarin mulki sai a yi zabe.

 

Kungiyar ta bayyana ta bakin kakakinta, Dr. Hakeem Baba Ahmad cewa, daga zabe zai zama katsalandan ga dimokradiyyar Najeriya dan haka basu yadda ba.

Karanta wannan  Kalli hoto:Shahararren dan daudu me saka kayan mata, Bobrisky ya fito takarar shugaban kasa

 

Hakanan shima kakakin kungiyar kare muradun inyamurai ta Ohaneze Indigbo, Chief Alex Nwokedi ya bayyana cewa, basu yadda da daga zaben ba.

 

Sannan kuma yace suna son shugaba Buhari ya kammala zabensa amma a bar inyamuri ya zama shugaban kasa a shekarar 2023.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.