fbpx
Thursday, July 2
Shadow

Bamu yadda da NCDC ba yaudarar Najeriya kawai suke>>jihar Kogi

Jihar Kogi da a karin farko ta samu mutane 2 masu dauke da cutar Coronavirus/COVID-19 wanda amma tace bata yadda da haka ba ta zargi hukumar NCDC da yaudarar ‘yan Najeriya.

 

Kwamishinan watsa labarai na jihar,Kingsley Fanwo ne ya bayyana haka a ganawar da yayi da gidan talabijin din Channelstv kamar yanda Hutudole ya samo.

Fanwo yace NCDC na da aniyar sai ta ga cutar Coronavirus/COVID-19 ta shiga kowace jiha a kasarnan sannan kuma tana so a rufe Najeriya gana daya.

 

Yayi zargin cewa NCDC yaudarar ‘yan Najeriya kawai take, jihar su bata da Coronavirus/COVID-19 amma sai da hukumar ta yi kutin-kutin aka sami cutar a jihar, gashi tattalin arziki ya shiga wani hali.

 

Ya kara da cewa ga cututtuka da yawa nan na kashe mutane, misali Malaria ta kashe mutane fiye da Coronavirus/COVID-19 a watanni 2 da suka gabata amma NCDC ta fi maida hankali kan cutar.

 

Ya kara da cewa, su fa basu yadda da hukumar ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *