fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Bamu yadda da taron da aka yi ba, ya sabawa doka>>Bangaren dake goyon Bayan Oshiomhole na APC zasu garzaya kotu

Bangaren jam’iyyar APC dake goyon bayan tsohon shugabanta, Adams Oshiomhole sun bayyana cewa taron jam’iyyar da aka yi jiya a fadar shugaban kasa wanda shugaba Buhari ya jagoranta bisa tafiyar sabon shugaban riko na jam’iyyar,  Victor Giadom ya sabawa doka.

 

Mutanen su 18 sun ce babu inda dokar jam’iyya tace mataimakin sakatare ya zama shugaban jam’iya kuma idan za’a yi taro irin wannan sai an bada akalla tazarar kwanaki 14 ba irin yanda aka yi yanzu ba.

Sun ce dan haka suna tattaunawa da Lauyoyinsu dan sanin matakin da ya kamata su dauka nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.