fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Ban ce bani tare da ku ba>>Mawaki Davido yawa masu zanga-zangar SARS karin haske

Mawaki Davido da aka zarga da nesanta kansa da zanga-zangar SARS a lokacin ganawa da shuvaban ‘yansanda, yayi karin haske inda yace ba’a fahimceshi ne ba.

 

Ya bayyana hakane ta shafinsa na sada zumunta inda yace an masa mummunar fahimtane. Yace shine da kansa yasa a rika daukarsa kai tsaye a wajen ganawar dan mutane su ga abinda ke gudana.

 

Yace an tambayeshine yaya aka yi aka ganshi da masu zanga-zanga bayan da shi ga abinda ya kawoshi ya gana da shugaban ‘yansanda? Yace shine yake bayanin cewa yana tare da duk ‘yan Najeriya amma ba zanga-zangar tada hankali ya je yi ba.

Karanta wannan  Inyamurai basu shirya shugabancin Najariya ba>>Inji Kwankwaso

 

Ya kuma kara da cewa, yana tare da masu zanga-zangar kuma masu yada labarin karya akansa kamata yayi a irin wannan lokaci, hankalinsu ya koma kan yanda za’a shawo kan matsalar da ake ciki.

 

View this post on Instagram

I am Nigerian first before anything ..

A post shared by Davido Adeleke (@davidoofficial) on

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.