fbpx
Saturday, September 19
Shadow

Ban cewa sojoji su dawo min da makaman da aka kwace ba>>Gwamna Ortom

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya bayyana cewa bai bukaci sojoji su dawo masa da makaman da aka kwace daga hannun ‘yan Bindiga ba.

 

Gwamnan ya bayyana hakane ta bakin kakakinsa, Terver Akase inda yace Maganar Gaskiya shi bai ce sojoji su dawo masa da makaman da suka kwace a hannun ‘yan Bindiga ba.

Yacw abinda ya bukaci a dawo dasu shine motar gwamnati wadda ta shugaban karamar hukumar Katsina ala ne wanda Terwase Agwaza, Gana na ciki yayin da sojojin suka tafi dashi.

 

Yace hakanan kuma akwai takardu a cikin motar wanda sune yace a dawo masa dasu sannan kuma da sauran tubabbun ‘yan ta’addan dan kammala tiban da suka yi.

 

Gwamnan yace me zai yi da makaman ‘yan ta’addar, bayan a shekarar 2015/2016 ya lalata wanda tubabbun ‘yan bindigar suka mikawa gwamnati a Idon duniya, dan haka wannan kawai karyace.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *