Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya bayyana cewa, bai ji dadin kisan mutanen da aka yi a jihar Filato ba.
‘Yan Bindiga sun kashe mutane akalla 80 a Kanam dake jihar ta Filato.
Gwamnan Bauchi da yake magana akan lamarin ta shafinsa na sada zumunta, yace idan aka taba mutum daya kamar an taba kowane.
Yace ya damu da kisan da aka yi sannan kuma ya bada shawarar ganin hakan ba ta sake faruwa ba da kuma hukunta wanda suka yi wannan danyen aiki.
Every Nigerian life matters, and the first way to prove this is to ensure these dastardly acts are never allowed to happen! The second way is to ensure maximum consequences for any cowardly action or attack.
— Senator Bala A. Mohammed (@SenBalaMohammed) April 12, 2022
A karshe ya mika sakon ta’aziyyarsa ga jama’ar Jihar Filato.