Babban faston RCCG Adeboye ya karyata rahotannin dake bayyana cewa ya kaddamar da Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.
Inda rahotannin suka ce ya gana faston ne kan tsayar da Musulmi dan uwansa daya yi a matsayin abokin takararsa.
Rahotanni da dama sun bayyana cewa babban faston ya kaddamar dashi bayan dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar APC ya kai masa ziyara a coci.
Amma yanzu cocin ta bayyana cewa fasto Adebayo bai kaddamar dashi ba kuma ba zai taba kaddamar da wani dan siyasa ba domin shi Allah yakewa aiki ba ‘yan siyasa ba.