fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Ban nada Sanusi a matsayin Sarkin Kano don na bata wa Jonathan rai ba>>Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, ya musanta nada wani tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Muhammad Sanusi II a matsayin Sarkin Kano don ya batawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan rai.

 

Kwankwaso ya mayar da martani ne ga kalaman da Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje yayi inda yace Kwankwaso ya nada Sanusi II don ya batawa tsohon shugaban kasa Jonathan rai.

A lokacin da yake gabatar da wani littafi a kan Jonathan, Ganduje ya ce Sanusi ba shi ne mutumin da ya fi dacewa da gadon sarauta ba a lokacin da aka nada shi a watan Yunin 2014, yana mai cewa an nada Sarkin da aka tsige ne domin ya batawa tsohon Shugaban kasar rai.

 

Gwamnan ya kuma ce an cire Sanusi daga mukaminsa domin ya ceci tsarin da kuma cibiyoyin gargajiya.

Karanta wannan  Gwamnatin jihar Ondo zata baiwa duk wanda ya kawo mata labaran sirri na 'yan bindiga naira dubu hamsin

 

Duk da haka, Kwankwaso a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Babban Sakataren sa na Musamman, Muhammad Ali, ya bayyana cewa nadin sarautar da aka yi wa Sanusi a matsayin Sarkin Kano anyi shi ne akan tsarin da ya dace kuma an yi shi tare da dokar masarautar ta Kano.

 

Tsohon gwamnan ya kara da cewa an zabi Muhammad Sunusi II ne a tsakanin sauran wadanda suka fafata domin shi (Sanusi) yafi son abunda mutane suke so, kuma yana ilimi a bangaren ilimin Islama da Boko.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.