Me magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya bayyana cewa dalilin da yace basu amfani da jiragen Super Tucano wajan kashe ‘yan Bindiga shine suna bin sharudan da kasar Amurka ta Gindaya musu ne kamin ta sayar musu da jiragen.
Ya bayyana hakane a wajan tattaunawar da gidan talabijin na Trust TV yayi dashi.
Yace basu son Najeriya ta shiga cikin bakin littafin kasar Amurka.
Sannan basu son shugaban kasa, Muhammadu Buhari idan ya kammala mulki a kaishi kotun Duniya ta ICC.
Yace abinda suke so shine idan ya kammala mulki, ya koma Daura ko Kaduna ya huta.
Yace dalili kenan da yasa aka bar sojoji su yi amfani da dabarunsu na yaki wajan gamawa da ‘yan Bindigar.
Yace idan mutum na hulda da kasa irin Amurka, dolene sai ya kiyaye ra’ayoyin jama’a akan abinda yake, saboda kasar na daukar ra’ayoyin jama’a da muhimmanci sosai.
Yace kada a manta fa, sai da aka dauki lokaci me tsawo, sannan sai da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tabbatarwa kasar Amurka za’a yi amfani da jiragen yanda ya kamata kamin aka amince aka sayarwa da Najeriya su.
Yace kasar Amurka bata son a yi amfani da irin wadannan jirage akan mutanen da takewa kallon farar hula.