A jiyane dai Shuwagabannin kungiyar dattawan Arewa ta bakin kakakinsu, Dr. Hakeem Baba Ahmad suka baiwa shugaba Buhari shawarar yin murabus.
Sun yi korafin cewa matsalar tsaron Najeriya ta nuna cewa shugaba Buhari ya gaza a mulkin kassrnan. Dan haka ya sauka kawai.
Hakan yasa an samu ra’ayoyi mabanbanta inda wasu ke goyon bayan hakan amma wasu basu goyi baya ba.
Cikin wanda suka bayyana ra’ayinsu akan wannan matsaya ta dattijan Arewa, akwai sanata Shehu Sani.
Sanata Sani ya bayyana cewa, kamata yayi a bar shugaba Buhari ya kammala wa’adinsa sai a yi sabon zabe.
Ya bayyana hakane ta shafinsa na sada zumunta.
Our respectable Northern Elders want Buhari to resign;I humbly disagree,allow Sai Baba to finish his tenure and conduct elections.