Mawakin kudancin Najeriya, Wizkid ya bayyana cewa, bai yadda da kowane addini ba.
Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda kuma ya kara da cewa, yawan shekaru ba shine ke nufin mutum na da basira ba.
Hakanan ya kara da cewa, shi babu abinda yake yadda ya dameshi, kuma baya rike mutane a zuciya.