Gwamnan jihar Kogi, Yahya Bello ya bayyana cewa, bai amince da sakamakon zaben fidda gwani na jam’iyyar APC ba.
Me kula da yakin neman zaben gwamnan, Mrs. Yemi Kolapo ne ya bayyana haka inda yace qn yi zaben cikin kwanciyar hankali da lumana amma ba’a yi gaskiya ba.
Ya kuma kara da cewa, kamata yayi a jinjinawa gwamna Yahya Bello wanda duk da tadiyeshi da aka so a yi, bai yadda yayi kasa a gwiwa ba sai da ya kai karshe aka buga zaben dashi.