Mawaki Davido na ci gaba da shan suka daga mabiyansa bayan bidiyo da aka dauka cikin sirri ya bayyanashi yana cewa baya cikin masu zanga-zanga a ganawar sirri da shugaban ‘yansanda yayi dashi.
Shugaban ‘yansandan ya tambayi David shin me yasa ya shiga Zanga-zangar saidai yace bai shiga ba, kawai dai ya jene ya kwantarwa da masu zanga-zangar hankali saboda masoyansa ne.
Bayan kammala ganawa da shugaban ‘yansandan, Davido ya bayyana cewa an bashi damar ya je ya kafa kwamitin sa ido akan horo na musamman da za’a baiwa ‘yansandan sabuwar Rundunar yaki da laifuka da za’a kafa.