fbpx
Friday, August 12
Shadow

Bana garkuwa da mutane aika su barzahu kawai nake yi, cewar shugaban ‘yan bindiga na jihar Zamfara

Shugaban ‘yan ta’addan jihar Zamfara da aka baiwa sarauta kwanakin nan, Adamu Aleiru ya bayyana cewa shi baya garkuwa da mutane sai dai ya aika su lahira.

Ya bayyana hakan ne yayin dayake ganawa da manema labarai, inda ya bayyana masu cewa yaran shi dai suna yin garkuwa da mutane amma shi sheke su kawai yake yi.

A makon daya gabata ne sarkin Yandoto ya baiwa Aleiro sarautar shugaban Fulani, amma gwamna Matawalle ya kalubalanci hakan inda har ya dakatar da sarkin da yayi wannan nadin.

Karanta wannan  'Yan bindiga sun kai hari Illela sun kashe mutane 11 sunyi gakuwa da mutanen da ba a san adadin su ba

Domin yace Alero har yanzu hukuma na nemansa kuma an saka kudi har naira miliyan biyar duk wanda ya kamo shi.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.