Gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ya bayyana cew baya tsoron duk wa’yanda ke neman takarar shugabancin Najeriya karkashin tutar APC.
Wasu daga cikin masu neman takarar shugabancin karkashin jam’iyyar APC sun hada da tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu da mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo.
Amma duk da haka Bello Yahaya ya bayyana cewa baya tsoronsu kuma yanada yakinin cewa shine zai yi nasarar lashe zaben a shekarar 2023.