fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Bani na dauki Maryam Booth Hoto Tsirara ba>>Deezell

A karo na 2, tauraron mawaki, Ibrahim Rufai wanda aka fi sani da Deezell ya sake yin magana akan dambarwar dake tsakaninshi da tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Booth akan fallasar hoton bidiyonta tsirara.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Deezell a sakon daya fitar ta shafinshi na sada zumuntar Twitter ya bayyana cewa maganar da Maryam Booth ta yi na cewa wai shine ya dauke ta hoto Tsirara ba da son ranta ba, ba gaskiya bane.

Ya kara da cewa hakanan maganar wai ya kuma rika amfani da bidiyon yana karbar kudi a hannunta shima duk ba gaskiya bane. Yace idan kuma tana da hujja akan hakan sai ta gabatar.

Deezell yace tabbas shi tsohon saurayintane amma bashine ya dauketa hoto tsirara ba.

Deezell yace a ‘yan kwanakinnan an ta yi mai kalaman kiyayya dana tsokana dana tunzurawa a shafukanshi na sada zumunta amma duk bai nuna damuwa ba inda yace amma a wannan karin abin ya tabashi inda ya bata mai rai.

Karanta wannan  Ka fadawa mabiyanka su daina min kazafi, Tinubu ya fadawa Peter Obi

Yace an yi wannan abune kawai dan a bata mai suna a wajan iyalanshi, yace ya rika samun kiraye-kirayen waya da sakonni da yawa akan wannan lamari.

Deezell ya bayyana cewabyana bukatar Maryam data janye wannan zargi data ke mai kuma ta bashi hakuri.

Ya kara da cewa ya gabatar da wannan lamari gaban masu bashi shawara kan shari’a inda zasu bashi shawarar abinda ya kamata yayi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.