fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Bani na nemi a bani sarautar da ake ta cece kuce akanta ba, cewar kasurgumin dan bindigar jihar Zamfara

Kasurgumin dan bindigar jihar Zamfara, Adamu Aleiro ya bayyana cewa bashi ya nemi a bashi sarautar da mutane keta cece kuce akan ta ba.

Aleiro ya bayyana hakan ne yayin daya ke ganawa da manema labarai na DW Hausa, inda yace daga farko ma shi kin karbar sarautar yayi saida mutane suka ce ya ansa.

Inda kuma yace bashi ne ya kashe mutane dari da ake tuhumarsa da kashewa ba a kauye Kadisau na jihar Katsina, kawai an dora laifin akansa ne.

Karanta wannan  A rika sanar dani daga yau domin ba zan laminci kashe mutane a kudu maso gabashin Najeriy ba, cewar shugaba Buhari

A kwanan baya ne sarkin Yandoto ya baiwa Aleiro sarautar sarkin Fulanin yankin wanda hakan aka dakatar da sarkin, Aliyu Marafa kuma gwamnatin jihar ta bayar da umurni ayi bincike akan dalilin daya sa aka yi wannan nadin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.