fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Banki Musulunci yana da amfani sosai – Sanusi Lamido Sanusi

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Alhaji Muhammadu Sanusi, ya zargi wasu ‘yan Najeriya da yin amfani da addini domin a boye gaskiya.

Ya yi magana a kan cece-kucen da ya biyo bayan bullo da tsarin hada-hadar kudi da babu ruwa wanda aka fi sani da bankin Musulunci.

Sanusi, wanda ya kasance bako a wajen taron harkar kasuwanci na kasa a karo na 5, wanda kungiyar musulmi maza masu sha’awar kasuwanci da sana’o’i da suka gudanar a jami’ar Legas, ya ce babban bankin CBN ya yi kokarin bayyana wa mutane cewa babu wani abu kamar mayar da kirista Musulmai a cikin bankin Musulunci a kasar nan.

Sai dai ya ce babban bankin na CBN ba zai iya tsayawa ba saboda ‘yan kalilan din da suka ki sauraron bayanin bankin koli, yana mai cewa alfanun tsarin bankin Musulunci na da yawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.