fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Bankin Duniya Ya Amince Da Bada Dala Miliyan 500 Ga Ilimin ‘Yan Matan Najeriya

A ranar Laraba ne Babban Bankin Duniya ya amince da bayar da dala miliyan 500  don inganta damar karatun sakandare a tsakanin matasan mata a wasu yankunan kasar nan.
Babban bankin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya yi wa taken ‘Najeriya don bunkasa tallafi don kiyaye yan matan da ba su zuwa makaranta “.
Ya bayyana cewa ‘yan matan masu tasowa suna fuskantar matsaloli da yawa wajen samun damar kammala karatun sakandare.
A Arewacin Najeriya, karancin makarantun sakandare ya yi yawa sosai tare da kusan makarantun firamare 10 ga kowane makarantar sakandare.
Ya ce, “Karancin kayayyakin gine-gine masu kyau da kuma rashin tsabtatataccen ruwa da kuma wuraren tsabta ya sa ya zama da wahala yara mata su kasance a makaranta.
“Bugu da kari, kusan kashi 80 na talakawa gidaje suna cikin Arewa, wanda hakan ya basu matukar wahala su tabbatar da kudaden makaranta.
“Duk wadannan abubuwan sun ba da gudummawa wajen rage yawan matan da suka samu damar shiga makarantar sakandare.
“Idan ba a yi komai ba, ‘yan mata miliyan 1.3 daga cikin miliyan 1.85 da suka fara makarantar firamare a shekarar 2017/2018 a jihohin arewacin kasar za su bar karatun kafin su kai ga shekarar karshe a karamar makarantar sakandare.”
Babban bankin duniya ya ce aikin zai tallafa wa samar da ilimin sakandare da karfafawa yara mata a cikin jihohi bakwai wadanda su ne Kano, Kebbi, Kaduna, Katsina, Borno, Plateau da Ekiti.
Musamman, aikin zai amfana da matasa miliyan 6.7 da kuma masu cin gajiyar shirin kai tsaye miliyan 15.5 zasu hada da iyalai da al’ummomi a cikin yankunan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Zan iya rantsuwa da alkur'ani cewa Atiku ne ya lashe zaben shekarar 2019, cewar Buba Galadimar

Leave a Reply

Your email address will not be published.