Bankin Duniya ya bayyana cewa yana fatan Najeriya ta cimma burin ta na cire mutane Miliyan 100 daga talauci kamar yanda ta yi niyya.
Saidai yace akwai sharuddan da ya kamata gwambatin tarayya ta bi muddin tana son cimma wannan buri nata.
Yace kamata yayi a kula ilimin yara mata da kuma samar da ayyukan yi.
Wakilin bankin Duniya a Najeriya, Mr. Shuabham Chaudhuri ne ya bayyana haka yayin kaddamar da wani shirin ilimantar da yara mata.