fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Banson hada kasa da mutanen Arewa saboda tunaninsu dabanne da namu>>FFK

Tsohon Ministan Sufurin jiragen sama,  Femi Fani Kayode ya bayyana cewa bai yadda da Najeriya a matsayin dunkulalliyar kasa ba.

 

Ya bayyana hakane a wani Bidiyon da ke yawo a shafukan sada zukunta inda aka jishi yana gayawa me fafutukar kafa kasar Biafra,  Nnamdi Kanu cewa shugaba Buhari ya taba ce masa ba zai taba yadda da Inyamuri ba.

 

Yace shugaban ya gaya masa hakane a wata ganawa da suka yi. Yace dalilin da shugaba Buharin ya bashi shine cewa, Iyamurai sun kashe shuwagabannin Arewa dan haka ba abin yadda bane.

Karanta wannan  Hotuna: Yanda aka yi Jana'izar Sakataren OPEC, Muhammad Barkindo

 

Hutudole ya fahimci cewa, A cikin Bidiyon da ya watsu sosai a shafukan sada zumunta wanda tun shekarar 2017 aka daukeshi, Fani Kayode ya kuma bayyana cewa, bai son hada kasa da mutanen Arewa maso gabas dana Arewa maso yamma saboda tunaninsu akan Duniya dabanne da na mutanen kudu.

 

“They killed our leaders. And we can never forget it. It is a cultural problem. You can’t trust them.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.