Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da cewa akwai barayi a cikin gidan gwamnatin ta bangaren dakin ajiya na asusu.
Darekta janar na gidan, Alhaji Al’amin Isa ne ya bayyana hakan yayin dayake ganawa da manema labarai.
Alhaji Al’amin bai bayyanawa manema labarai ko nawa ne aka sace ba amma yace wa’yanda ake zargi da satar suna ofishin hukumar ‘yan sanda.
Yayin da wani daga cikin gidan gwamnatin ya bayyanawa manema labarai na Daily Independence cewa naira miliyan 31 ce aka sace.