fbpx
Friday, July 1
Shadow

Barayi sun shiga gidan dan wasan Liverpool, Fabinho yayin da suke bikin lashe kofin Premier League

Barayi sun shiga cikin gidan dan wasan Liverpool Fabinho wanda ya kasance dan kasar Brazil tsakanin karfe uku na yammacin ranar laraba 22 ga watan yuli zuwa karfe 4 na safiyar ranar alhamis 23 ga watan yulin.

Yan sandan garin Merseyside sun sanar cewa barayin sun saci kayan alatu a gidan dan wasan tare da Motar Audi RS6 yayin da suke gunadar da aika-aikar tasu a Formby. Kuma daga baya anga motar a yankin Wigan.

Fabinho bai san komai gami da lamarin ba har saida ya koma gida bayan sun ba Chelsea kashi a filin su har 5-3 kuma suka daga kofin gasar premier league karo na farko tun bayan shekaru 30 da suka gabata, tsohon tauraron Kungiyar Sir Kenny Dalglish shine ya gabatar masu da kofin.

Karanta wannan  Shalelen PSG, Mbappe ya cewa kungiyar ta sayar da Neymar don baya cikin tsarinsa

Wani jami’in dan sandan garin Merseyside yace an kira ofishin su da safiyar ranar alhamis 23 ga watan yuli yayin da wani magidanci ya shiga gidan shi kuma ya fahimci barayi sun yi mai sata, zasu cigaba da gudanar da bincike gami da lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.