fbpx
Friday, July 1
Shadow

Barayi sun shiga gidan Ribery yayin da yake bugawa Fiorentina wasa wanda suka yi nasarar tashi 2-1

An yiwa tsohon tauraron Bayern Munich fashi a gidan shi Franck Ribery yayin da yake bugawa kungiyar Fiorentina wasa a yammacin ranar lahadi, wanda hakan yasa ya fara yin kokwanton cigaba da wasa a kasar italiya.

Barayin sun yi mai satar agogon Rolex guda biyu da sarkar gwal guda goma sai suka yiwa matar shi jaka guda goma kuma suka hargitsa gidan kafin su fiche. Kuma Rjbery yace a yau taya zamu ringa yarda da mutanen da meke zama dasu?.

Dan wasan mai shekaru 37 ya wallafa bidiyon yadda barayin suka yiwa gidan shi a Instagram, kuma ya fara saka rayuwar iyalan shi farko kafin maganar aukuwar lamarin. Yayin da yake cewa kalli yadda barayi suka yiwa gidan shi a kasar Italiya wadda ya zabi ya cigaba da wasa bayan Munich.

Karanta wannan  Shalelen PSG, Mbappe ya cewa kungiyar ta sayar da Neymar don baya cikin tsarinsa

Ya kara da cewa yana godiya ga Allah saboda bai rasa komai ba, kuma ba farautar miliyoyi yake ba shi farautar kwallaye yake yi saboda hakan ra’yin shine. Kuma iayalan shi suna gaba da ra’ayin shi saboda haka zasu yanke shawarar data kamata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.