Tauraron dan wasan Barcelona mai shekaru 17, Ansu Fati wanda yanzu ya samu damar shiga tawagar farko kuma aka bashi lamba 22 yayi nasarar cin kwallaye biyu a wasan Barcelona na farko a gasar La Liga na wannan kakar, kuma dan wasan Sifaniyan shine yasa Barcelona tayi nasara akan Villarreal.

Ansu Fati ya zamo dan wasan daya fara ciwa Barcelona kwallo a wannan kakar sannan kuma ya zamo dan wasa na shida a gasar La Liga wanda ya ciwa kungiyar shi kwallo ta farko a gasar yana dan kasa da shekara 18. Fati ya haskaka sosai a wasan saboda cikin mintina 20 ya zira kwallaye biyu kuma a minti na 34 yayi sanadiyar penaritin da Messi yaci.
Pedri da Trincao da tsohon dan wasan Juventus Pjanic duk sun fara bugawa Barcelona wasa a yau, yayin da Pedri ya canji Coutinho a minti na 69 kafin Trincao ya canji Griezmann kuma Pjanic ya canji Sergio a minti na 79. Dan wasan Villarreal Pau Torres shiine yai ciwa Barcelona kwallon su ta karshe a wasan ana gab da zuwa hutun rabin lokaci.