fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Barcelona 5-0 Alaves: Messi yaci kwallaye biyu a wasan yayin daya gama wannan kakar da kwallaye 25

A yau Barcelona suka gama buga kakar wasan su na 2019/20 da ci biyar da suka wa kungiyar Alaves. Barcelona sun kwashi abun kunya a gidan su a wasan daya gabata wanda Osasuna suka cisu 2-1, yayin da su kuma abokan hamayyar su Madrid suka daga kofin La Liga a ranar.

Tauraron dan wasan su mai karancin shekaru Ansu Fati ne ya fara cin kwallon a wasan, sai kaftin din su Messi yaci kwallo guda kafin Luiz Suarez da Nelson Samedo suci nasu kwallayen. Messi ya kara cin kwallo bayan an dawo daga hutun rabin lokaci wadda tasa ya gama buga wannan kakar a kwallaye 25.

Barcelona sun gama buga wannan kakar da maki 82, kuma wannan ya kasance makin su mafi karanci tun kakar 2017/08. tsohon kochin su Valverde shine yaci masu maki 40 a wasanni 19 sai sabon kochin nasu Setien yaci masu maki 42 shima a wasanni 19. Messi shine zai lashe kyautar dan wasan da yafi cin kwallaye masu yawa a gasar La Liga yayin da kwallayen nashi suka kai 25.

Karanta wannan  'Yan wasan Manchester sun bukaci a sayar da Ronaldo kuma har yanzu baya jituwa da sabon kocin kungiyar

Benzema shine yake bin Messi da kwallaye 21 amma da kyar ya iya kerewa Massi saboda wasa daya ne kacal ya rage masu wanda zasu buga da Leganes a yau, saboda haka messi ne zai lashe kyautar Pichichi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.