fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Barcelona ta bayyana cewa tauraron dan wasanta Ansu Fati zai dauki tsawon watanni hudu yana jinya bayan ya samu rauni a kafar sa ta hagu

Tauraron dan wasan Barcelona mai shekaru 18, Ansu Fati ya samu rauni a kafar shi ta hagu yayin da suke karawa da Real Betis jiya wanda suka yi nasarar lallasa kungiyar 5-2 a gasar La Liga.

Kuma kungiyar Barcelona ta sanar a ranar litinin cewa an yiwa tauraron dan wasan nata tiyata a kafar tasa kuma sai ya dauki tsawon watanni hudu yana jinya, wanda hakan ka iya kawowa Barca cikas a gasar zakarun nahiyar turai da kuma La Liga.
Ansu Fati yayi nasarar cin kwallaye biyar kuma ya taimama wurin cin kwallye biyu a wasanni goma daya bugawa Barcelona a wannan kakar, Amma yanzu raunin daya samu yasa ba zai buga wasan sada zumunta tsakanin Sifaniya da Netherland ba,kuma zai rasa wasannin da Sifaniya zata kara da kasar Switzeland da Jamus a gasar kofin kasashen nahiyar turai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Kungiyar PSG ta kori kocinta Maurizio Pochettino

Leave a Reply

Your email address will not be published.