Kungiyar Rayo Vallecano tayi nasarar lallasa Barcelona daci daya mai ban haushi a gasar La Liga ta hannun Garcia, wanda hakan yasa Barca ta fadi wasannin gida uku a jere karo na biyu a tarihi.
Rayo Vallecano ta zamo kungiya ta hudu data fito daga gasar Segunda kuma tayi nasarar cin gabadaya wasanninta na kaka tsakaninta da Barcelona a gasar La Liga.
Kuma kocin kungiyar Iraola shima ya zamo koci na farko a tarihi dayaci Barcelona a guda da waje a kaka guda.