fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Barcelona ta yiwa PSG tayin Fan miliyan 32 da Coutinho da Dembele a basu Neymar

Tauraron dan kwallon kasar Brazil Neymar ya koma kungiyarshi ta PSG dan fara Atisaye bayan da yayi lattin komawa da sati daya. Neymar ya koma PSG ne a jiya, Litinin inda bayan komawar tashi suka yi zama na musamman da daraktan wasanni na kungiyar, Leonardo de Araújo, kamar yanda kabarin wasanni suka bayyana.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A ganawar tasu, an ci tarar Neymar saboda bata lokacin da yayi wajan dawowa kungiyar sannan shima ya kara jaddadawa kungiyar cewa shifa yana so ya barta baiso ya ci gaba da buga musu wasa.
Labarin wasannin kamar yanda Le Parisien ta ruwaito sun ci gaba da cewa, Leonardo ya kara tunawa Neymar cewa kada ya mantafa yana da alkawarin yiwa PSG wasa akanshi wanda kuma dole ya girmamashi.
Neymar dai be bayyana cewa Barcelona yake son komawa ba.
A wani labarin wasannin da ya shafi Neymar da AS ta ruwaito kuwa ta ce ana cinikin da bana kai tsaye ba tsakanin PSG da Barcelona akan sayen Neymar inda a hukumance babu cinikin amma akwai dillalai dake tattaunawa a madadin kungiyoyin biyu ta bayan fage.
Barcelona ta yiwa PSG tayin Neymar ta hanyar basu Fan miliyan 32 da Philippe Coutinho da Ousmane Dembele akan Neymar din saidai PSG kwata-kwata taki amincewa da wannan tayi inda tace kudin da ta sayi Neymar Yuro miliyan 222 take so a dawo mata dasu, kamar yanda labarin wasannin suka nunar.
A yanzu dai Barcelona bata da wannan kudi dan kuwa sai da ta ciwo bashi sannan ta samu siyo Griezmann daga Atletico Madrid akan fan miliyan 120.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Zan iya rantsuwa da alkur'ani cewa Atiku ne ya lashe zaben shekarar 2019, cewar Buba Galadimar

Leave a Reply

Your email address will not be published.