fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Barcelona tayi burus da tayin da aka yiwa Ansu Fati na yuro miliyan 150

Sabon wakilin Ansu Fati Jeorge Mendez shine ya sanar da Barcelona wannan kwantirakin na yuro miliyan 125 tare da karin yuro miliyan 25 idan dan wasan yayi kokari sosai amma Barcelona tayi burus da wannan tayin kuma taki amincewa ta fara tattaunawa akan siyar da dan wasan mai shekaru 17.

A farkon wannan shekarar wata kungiya ta taya Ansu Fati a farashin yuro miliyan 100 kuma shima wannan tayin ta hannun Jeorge Mendez ya fito duk da cewa a lokacin ba shine wakilin dan wasan ba, amma Barcelona taki amincewa da siyar da dan wasan Sifaniyan kuma har ta saka mai farashin yuro milyan 400 domin kar wata kungiya tayi yunkurinn siyan shi.
Mendez bai bayyana sunan kungiyar data taya Ansu Fati a farashin yuro miliyan 150 amma an samu labari daga kasar Ingila cewa Manchester United tana da ra’ayin siyan dan wasan musamman domn ta fafata da Manchester City da Chelsea da kuma Liverpool a gasar Premier League.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Cristiano Ronaldo na son barin Manchester United ne saboda Lionel Messi, karanta kaji dalili

Leave a Reply

Your email address will not be published.