fbpx
Friday, February 26
Shadow

Barcelona zata mayar da sunan filin wasanta Lionel Messi

Emili Rousaud, wanda yake neman takarar kujerar shugabancin kungiyar Barcelona ya bayyana cewa zai canja sunan filin kungiyar daga Camp Nou ya koma shi Lionel Messi idan har aka zabe shi a watan janairu.

Bayan canja sunan filin kungiyar da zai yi ya kara da cewa zai dawo da Neymar Barcelona sannan kuma zai kara siyo wani tauraron dan wasa a kaka mai zuwa idan har yaci zaben.

Sabon kocin Barcelona Ronald Koeman ya kasa jagorancin kungiyar yadda ya kamata yayin da har yanzu Messi bai sabunta kwantirakin shi ba kuma zai bar kungiyar kyauta da zarar kwantirakin shi ya kare nan da kaka mai zuwa.

Amma duk da haka Emili yana ganin cewa zai iya shawo kan tauraron dan wasan Argentinan ya cigaba da wasa a Barcelona ta hanyar mayar da sunan filin kungiyar Lionel Messi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *