fbpx
Monday, August 8
Shadow

Barin shan taba da Shan giya da motsa jiki na karawa mutum tsawon rayuwa da shekaru 8>>Masana

Masana daga jami’ar Leicester dake kasar Ingila sun bayyana sakamakon wani bincike da suka gudanar da ya nuna cewa barin shan taba sigari da barin shan Giya da kuma yawan motsa jiki na kawarawa mutum tsawon rayuwa da shekaru 8.

 

Binciken yace hakan kuwa na faruwa ga mutum ne koda yana da wani ciwo me tsanani kamar su, ciwon Suga, Ciwon Zuciya, Ciwon Kansa, Asama da dai sauransu.

Masanan sun yi amfani da bayanan mutane 480,000 da aka tattara daga gurare daban-daban da jinsi daban-daban aka kuma bibiyi yanda suke gudanar da rayuwa.

Karanta wannan  Kalidou Koulibaly da Raheem Sterling sun bugawa Chelsea wasan Premier league na farko da kafar dama

 

Daya daga cikin wanda suka yi binciken, Yogini Chudasama ta bayyana cewa mutanen da suka bar shan Taba, suka bar shan Giya sannan suka rika motsa jiki da cin abinci me kyau zasu samu karin tsawon rayuwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.