fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Bashir Tofa cikakken ɗan kishin ƙasa ne>>Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya miƙa ta’aziyyar rasuwar tsohon ɗan takarar shugabancin ƙasar Bashir Tofa ga iyalai da gwamnati da kuma al’ummar Jihar Kano, yana mai bayyana shi a matsayin “cikakken ɗan kishin ƙasa”.

“Ha zuwa lokacin rasuwarsa, cikakken ɗan kishin ƙasa ne. Ya nemi kafa ingantacciyar Najeriya ga kowa da kowa,” a cewar Buhari cikin sanarwar da Garba Shehu mai magana da yawunsa ya fitar.

Sanarwar ta ƙara da cewa Shugaba Buhari ya yi addu’ar Allah ya ji ƙan sa sannan ya bai wa iyalai da abokansa haƙurin rashinsa. “Muna addu’ar aƙidarsa ba za ta gushe tare da shi ba,” in ji Buhari.

Karanta wannan  Labari me dadi: An kwato buhunan takin zamani da 'yan ta'adda suka siya dan hada bamabamai

Kazalika, Buhari ya tura tawagar ta’aziyya zuwa Jihar Kano da ta ƙunshi jami’an gwamnati da suka haɗa da ministan tsaro, ministan harkokin ruwa, babban akanta na ƙasa, da kuma Garba Shehu kakakin fadar shugaban ƙasa.

Bashir Othman Tofa ya rasu da asubahin Litinin yana da shekara 74 bayan ya sha fama da jinya kuma an yi jana’izarsa a birnin Kano.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.