fbpx
Sunday, June 26
Shadow

Batanci: CAN Ta Janye Gabatar Da Zanga-Zangar Da Ta Shirya Kan Kisan Deborah saboda Musulmai ma sunce zasu fito Zanga-Zangar

Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) ta bukaci mambobinta da su dakatar zanga-zangar da ta tsara yi ranar Lahadi kan kisan Deborah Samuel, dalibar da ta yi batanci ga Fiyayyen halitta (SAW) a Jihar Sakkwato.

Aminiya-Trust ta rawaito cewa, shugaban kungiyar na kasa, Dokta Samson Ayokunle ne ya ba da umarnin a cikin wata sanarwa ranar Asabar.

A maimakon haka, kungiyar ta bukaci Kiristocin su gudanar da zanga-zangar a cikin majami’unsu ranar Lahadi.

Shugaban ya ce, “Kuna sane da cewa wasu Musulmai sun shelanta shirya tasu zanga-zangar ranar Lahadi, 22 ga watan Mayun 2022. Babban burinsu shi ne su tayar da zaune tsaye sannan su alakanta hakan da mu.

“Saboda haka, ina kiranku da ku gudanar da zanga-zangar ta hanyar daga kwalaye a harabar majami’unku da sakatariyar CAN da ke yankunanku.

Karanta wannan  "Dalilin dayasa muka cire sunan Ahmad Lawal, Godwill Akpabio da gwamna Umahi a jadawalinmu">>INEC

“Sai dai a inda nan ma kuka fuskanci akwai matsala in kuka yi zanga-zangar a harabar majami’un naku, za ku iya daga kwalayen kawai a ciki, sannan ku yi wa Deborah Samuel addu’a.

“Sannan ku yi addu’a ga wadanda suke jin dadin kisan mutane ’yan uwansu da sunan addini,” inji Shugaban kungiyar Kiristocin.

Ya kuma bukaci majami’un da su kyale gidajen talabijin su dauki zanga-zangar sannan su yada ta a kafafen sada zumunta na zamani saboda duniya ta gani.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.