fbpx
Friday, June 9
Shadow

Batanci ga Fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) A Sokoto>>Ji Yanda abin ya faru Dalla-Dalla

Rahotanni daga Jihar Sokoto a Najeriya na cewa wasu da ake zargin ɗalibai ne a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari sun tayar da tarzoma bayan da aka zargi wata daliba da yin saɓo, abin da ya fusata ɗalibai suka shiga cinna wuta da hayaniya a makarantar.

Rahotanni sun ce har an yi asarar rayuka sakamakon wannan lamari, sai dai babu tabbaci daga hukumomi kan lamarin.

Tun bayan da aka soma wannan hayaniya aka tura sojoji da jami’an kwantar da tarzoma zuwa kwalejin ilimin domin kwantar da tarzomar.

Ko da BBC ta tuntuɓi rundunar yan sanda reshen Jihar Sokoto, mai magana da yawun rundunar ASP Sanusi Abubakar ya ce jami’an da suka tura sun kwantar da tarzomar kuma komai ya lafa.

Yadda lamarin ya faru

Wani ɗalibin kwalejin da BBC ta tuntuɓa ya bayyana cewa a lokacin da ɗaliban suka samu labarin faruwar lamarin, rigima sai ta kaure a cikin makarantar.

A cewarsa malamai da sauran shugabannin kwalejin sun yi ƙoƙarin su dakatar da ɗaliban daga wannan tarzoma amma abin ya ci tura, inda har jami’an tsaro suka je makarantar suna harba wa ɗaliban hayaƙi mai sa hawaye.

Ɗalibin ya bayyana cewa idan aka harba hayaƙin sai ɗaliban su ma su ɗauka su jefa wa jami’an tsaron. Ya ce ba ɗaliban kwalejin bane kaɗai suka tayar da hargitsin har da na waje suka shiga cikin kwalejin.

A cewarsa, wadda ake zargi da aikata saɓon an ɓoye ta a ɗakin jam’ian tsaro da ke ƙofar kwalejin inda masu tarzomar suka sha ƙarfin jami’an tsaron suka ɓalla ƙofar ɗakin suka ciro yarinyar.

Ya ce an yi ƙone-ƙone da farfasa muhimman kayayyaki a cikin kwalejin musamman motocin malamai.

Me jami’an tsaro suka ce

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Sokoto ta tabbatar da faruwar wannan tarzoma sai dai ba ta yi ƙarin bayani kan abubuwan da suka faru ba inda suka ce suna gudanar da bincike.

ASP Sanusi Abubakar wanda shi ne mai magana da yawun ƴan sandan ya ce ƴan sandan tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro sun bazama a yankin kuma a yanzu akwai kwanciyar hankali.

Ya ce ba su da tabbaci kan maganganun da ake yi na cewa wasu sun rasa ransu haka kuma bai tabbatar da ko an kama wani daga cikin masu tarzomar ba.

Bugu-da-kari ASP Sanusi yace idan akwai wani karin bayani musamman daga binciken da suke yi za su sanar nan gaba.

Tuni dai hukumomin kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto suka sanar da rufe makarnatar har sai abin da hali yayi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *