fbpx
Tuesday, March 28
Shadow

Bautar da bakar fata a kasar Libya: Ga wani jawabi da zai amfaneka

‘Yan kwanakinnan hankalin Duniya ya karkata zuwa kasar Libya tun bayan da aka samu rahotannin bautar da mutane, bakar fata dake zuwa kasar cirani ko kuma suke bi ta kasar dan zuwa wasu kasashen turai amma su makale.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

An samu hotuna masu tayar da hankali dake nuna yanda ake bautar da bakar fata.

Gwamnatin Najeriya ta dauki matakin dawo da wasu ‘yan ciranin ta hanyar aikawa da jirgi dan ya kwaso su.
Ga ra’ayin wata mata akan wannan batu da zai anfanar da duk wanda ya karantashi.
“Mai Martaba wannan Matsala ta Safara da cin zarafin baqar fata ba sabuwa ce, Sai dai bayyanar ta qarara a qasar Libya a wannan yanayi ba abin Mamaki bane. Sakamakon Yaqi, A halin Yanzu Qasar Libya ba ta da tsayayyar Gwamnati ko Tsayayyar Doka saboda haka babu tsoron aikata Laifi a fili domin akwai nutsuwar Rashin samun hukunci. Har Manyan Qasashen Turai da na Larabawa kamar Italiya da Saudiyya akwai Rahotanni marasa dadi dake fitowa, kwanan nan aka binne ‘yan Najeriya 26 a Italiya babu wani cikakken bayani da hukumomin Najeriya zasu iya bayarwa game da Yadda aka yi suka mutu, ko dalilin Gaggawar Binne su ba da sanin Jakadan Najeriya da ke can ba. Haka fa Rayuwar Dan Najeriya take, ko a Qasarsa ko a wata Qasar, in dai ba Wane ko d’an wane ba to ba shi bambanci da Kiyashi.
Ana samun Labaran yadda ake Safarar mata zuwa Saudiyya ta hanyar wasu kamfuna don su zama Masu aikin gida, Ko da abin ya tsaya a aikin gidan kawai a kan shiga cin zarafi na duka da zagi da wulaqanci, in abin Ya zurfafa har da fyade. Kwanakin baya na ga Labarin wata mata da Mai gidan da take aiki da ‘Dan sa ke neman yi maya fyade, ta yi iyaka qoqarinta ta nemi haqqinta ta hanyar kai qara kamfanin da suka kai ta amma abin ya ci tura, Ita baqar fata ce, baquwa(ko ma baiwa a idon su) wadanda take qara kuwa ‘yan Qasa ne. Daga baya ta samu Dabarar yin Video duk wanda ya sake zuwa zai mata fyade tsakanin Uban da ‘dan, sai ga shi ta kama ‘dan a video, ta kai wannan Video wancan Kamfani da ya Kai ta da nufin a bata masanin shari’ar qasar ya taimaka mata ta kai qara ga hukuma, Sai kawai a ka na’do ta aka dawo da ita Najeriya.
Akwai rahoton da ya nuna Kaso mafi yawa na Karuwai Mata Baqaqen Fata a qasar Italiya ‘yan Najeriya ne. 
Dole ne Duniya ta tashi tsaye don magance wannan matsala, Qasashen Afirka kuma su yi qoqarin daidaita Al’amuransu, su Kyautata yanayin Rayuwar Al’ummarsu, Ita kuma Al’Ummarmu wajibinta ne ta sani cewa Hangen Dala ba shiga birni ba ne, kuma Guntun gatarin ka Ya fi Sari ka bani.”
Allah yasa mu dace.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Warware Rawani Sarkin Kano Abu Ne Mai Wuya

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *