fbpx
Thursday, June 30
Shadow

“Baya kaunar Musulmai kuma bai kamata a bashi wani mukami a gwamnatin tarayya ba”>>Kungiyar Musulmai ta gargadi Atiku kar ya zabi Wike a matsayin mataimakinsa

Kungiyar dake kare hakkin Musulmai ta MURIC ta gargadi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar akan zabar Nyesom Wike a matsayin abokin takararsa.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata wasikar da darektanta farfesa Ishaq Akintola ya rattabawa hannu.

Inda kungiyar ta bayyana cewa gwamnan jihar Rivers din, Wike na daya daga cikin Kirista masu girman kai kuma baya kaunar Musulmai sannan har ya mayar da jiharsa ta Kirista.

Kuma sunga alamar cewa kamar shine Atiku yake shirin dauka ya zama abokin takararsa, saboda haka ne suke garggadin jam’iyyar akan zabar shi kuma bai kamata a bashi wani a gwamnatin tarayya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.